• Wani rikici ya barke a tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan kungiyar Ansaru a lokacin da ‘yan bindigar su ka kaiwa ‘yan kungiyar ta Ansaru hari a Jihar Kaduna.
    Wasu da lamarin ya faru akan idansu sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai wa ‘yan Ansarun harin ne a lokacin da ‘yan Ansarun su ke yiwa mutane Da’awa a kauyen Damari wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane guda biyu.
    Ishaq Usman Kafai wanda ya kasance shugaba mai jagorantar kungiyar hadin kan masarautur Birnin Gwari ya bayyana wa manema labarai cewa da yawa sun karkashe junan su wanda ba a san adadin su ba.
    ya ce a yayin fadan na ‘yan ta’addan sun hallaka wasu leburori guda biyu.
    Shugaban ya kara da cewa musayar wutar ta ‘yan ta’addan ta haddasa konewar wani Asibiti mai zaman kansa da motoci biyu da kuma wani shago.
    Usman Kafai ya ce sun shafe awa daya su na yi,inda ‘yan Ansarun su ka fatattakin ‘yan bindigan.
    Bayan da ‘yan kungiyar ta Ansaru ta samu galaba akan mayakan sun bayyana wa mazauna yankin cewa su mallaki makamai domin su kare kansu daga batagari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: