A gobe Alhamis kungiyar masu gidajen burodi PBAN ta fadin Najeriya ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin fara yajin aiki na tsawon kwanaki hudu a fadin Najeriya.

Kungiyar za ta shiga yajin aikin ne sakamakon yawan hauhawar farashin kayan da su ke hada burodin wanda hakan ke kawo musu cikas a cikin sana’ar.
Shugaban kungiyar Emmanuel Onuorah da mai magana da yawun kungiyar Babalola Thomas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina chajin su kaso 15 cikin 100 na fulawar da ake kawowa Najeriya.

Shugabannin sun kuma bukaci hukumar NAFDAC da ke tabbatar da sahihancin abinci da magunguna da ta sassauta tarar Naira 154,000 da ta ke sanyawa wasu gidajen buradin da ba su chanja lalasin hukumar akan lokaci ba.

Kungiyar ta PBAN ta roki gwamnatin da sahale mambobin kungiyar su amfana da rance da babban bankin Najeriya ya ke bai wa masu kananan sana’o’i da matsakaita.
Kungiyar ta ce halin da ake ciki a yanzu a Najeriya na tashin farashin kayayyaki na neman kawo musu nakasu a cikin sana’ar.
Kungiyar ta ce mafi yawancin masu sana’ar asara su ke tafkawa a cikinta.