Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sandan kwantar da tarzoma biyar da wasu farar hula uku a kauyen Gatikawa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

‘Yan sandan kwantar da tarzomar an ce sun je jihar domin gudanar da wani aiki na musamman ne daga Kano.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Laraba inda ‘yan bindiga sama da 300 suka far wa al’ummar yankin tare da harbe-harbe don tsorata mazauna garin.

Daya daga cikin majiyar ta ce ‘yan bindigar sun hau babura suna bi gida-gida suna kwashe duk wani abu mai daraja da suka hada da kudi da kayan abinci.

Ya ce an kuma jikkata wasu mazauna yankin musamman wadanda ke kokarin tserewa daga hannun ‘yan bindigar.

Sannan mazauna yankin sun firgita bayan harin kuma tuni wasu mazauna garin suka koma garuruwan da ke makwabtaka da su saboda fargabar sake kai wani hari.

Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wannan wata da wasu ‘yan bindiga ke kashe jami’an ‘yan sanda.

A ranar 5 ga watan Yuli, wasu ‘yan bindiga sun kashe wani babban jami’in dan sanda mai kula da yankin Dutsin-ma Aminu Umar, tare da wani dan sanda daya da wasu fararen hula.

Leave a Reply

%d bloggers like this: