Rahotanni daga kasuwar waya ta Beirut a Kano wani gini hawa uku ya faɗo a yau.

Yayin da Matashuya ke tabbatar da sahihancin bayanin, shugaban kasuwar Alhaji Ibrahim Rabi’u Tahir ya tabbatar da lamarin.
Ya ce ginin ba a kammalashi ba kuma a halin da ake ciki ana kan bincike domin gano ko an rasa rayuka a sandin rushewar ginin.

Ya kara da cewar a yanzu ba su tabbatar da ko an rasa rai a sanadin rushewar ginin ba, amma zuwa nan gaba bayan kammala bincike zai sanar da mu halin da ake ciki.
