Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, yace Sanata Rabiu Musa ya ci amanarsa da mabiyansa inda yace wannan ne dalilin da yasa ya sauya jam’iyyar siyasa.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin zantawa da shirin Siyasa a Yau na gidan Talabiji na Channels.

Sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce shugaban tafiyar Kwankwasiyya da gangan yayi jinkirin tabbatar da yarjejeniyar da suka tsaya a kai kafin ya shiga NNPP har zuwa lokacin da INEC ta rufe karbar ‘yan takara.

Ya ƙara da cewa sun mika bukatun su ga jam’iyyar bayan sun koma tare da mabiyan sa kuma sun zauna da Sanata Rabiu Kwankwaso, ya mika bukata kuma ya amince da ita.

Shekarau ya kara da cewa bai yi mamakin ganin sunayen ‘yan takara ba da INEC ta fitar daga shugabannin jam’iyyar NNPP a jihar.

Ya kara da cewa, a ranar 14 ga watan Mayu cikin dare, ya ga sunayen da shugabannin jam’iyya suka fitar da hannu aka rubuta sunayen ‘yan takarar da mazabunsu.

Wannan na zuwa ne kasa da watanni uku bayan shekarau ya bar jam’iyyar APC inda ya koma jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: