Gwamnatin jihar Legas ta ce duk wanda aka samu da karya dokar Achaɓa a jihar za a ɗaureshi shekara uku a gidan gyaran hali.

Kwamishinan sufuri a jihar Frederic Oladinde ne ya sanar da haka jiya yayin ganawa da jami’an tsaro tare da sanar da su dokar da gwamnatin jihar ta samar a kai.
Oladinde ya ce dokar ta shafi masu babur ɗin haya da aka ɗauka da kuma wanda aka ɗauka da sunan fasinja.

Yayin da ya ke jawabi ga maenema labarai a dangane da hana achaɓa a jihar, Oladeinde ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin hakan ne domin kare ryuwar jama’ar jihar.

Bayan gwamnatin ta hana hayar baburan ta na ƙoƙarin samar da isassun motocin sufuri domin gamsar da jama’ar jihar a wuraren da aka hana bayar baburan.
Gwamnatin ta ɗora alhakin tabbatar da dokar hana achaɓa a kan jami’an tsaro kamar ƴan sanda, sojin sama, sojin ƙasa, sojin ruwa da sauran dukkanin masu alhaki a ɓangaren tsaro.
Oladeinde ya sake jaddada matsayar gwamnatin jihar n hana achaɓa baki ɗaya a wuraren da ta lissafa, kuma za domar ɗaurin za ta fara ne daga yau Alhamis.