Kwamitin majalisar dattawa mai kula da manyan makarantun kasar ya ce akwai bukatar a kara harajin manyan makarantu daga kashi 2.5 zuwa uku domin inganta bincike da ci gaba a kasar.

Kwamitin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar sa ido a Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) domin tabbatar da aikin kasafin kudin shekarar 2021/2022.

Kwamitin da Sanata Ahmed Babba Kaita ya jagoranta ya yi nuni da cewa bangaren ilimi da kiwon lafiya bangare biyu ne masu matukar muhimmanci da ke kawo ci gaba, don haka akwai bukatar a sake duba harajin ilimi.

Ya bukaci hukumar da ta sanya Cibiyar Lissafi ta Kasa (NMC) a cikin ayyukanta, tana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba a fannin bincike, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ba tare da rungumar ilmin lissafi ba.

Kaita ya kuma bukaci TETFund da ta kara himma wajen samar da injin samar da iskar oxygen da Polytechnic ta jihar Kaduna ta nema yayin annobar COVID-19 a shekarar 2020.

Tun da farko, Sakataren zartarwa na TETFUnd, Sonny Echono, ya ce a shekarar 2021, hukumar ta raba naira biliyan 213 ga manyan makarantu, ciki har da tallafi ga sabbin cibiyoyi.

Da yake amsa bukatar samar da injin samar da iskar oxygen na jihar Kaduna Polytechnic, Echono ya bayyana cewa asusun ya amince da Naira miliyan 50 don gudanar da bincike kuma an biya rabin kudin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: