Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kaddamar da makarantar Sakandire mai daukar mutane 1,500 a garin Buratai da ke karamar hukumar Biu ta jihar a jiya Talata.

Bayan bude makarantar da gwamnan yayi ya bayar da umarnin daukar sabbin malamai 20 ‘yan cikin kauyen a matsayin na Wucin gadi domin ganin kwarewar su kafin daukar su koyarwa ta dindindin.
Kwamishinan Ilmi na Jihar Injiniya Lawan Abba Wakilbe a yayin jawabin sa ya bayyana cewa shekaru uku da su ka shude gwamnan ya dauki malamai fiye da 1000 tare da basu horo domin kwarewa a fannin koyarwa a fadin Jihar.

Kwamishinan ya ce bayan bai wa malamai horo da aka yi aka turasu makarantun da ke fadin Jihar domin koyar da dalibai.

Injiniya Lawan Abba ya kara da cewa gwamnan ya gina manyan makarantu 24 daga bisani kuma ya bayar da umarnin gyara ajujuwa guda 600 a makarantu guda 100 tare da kaddamar da gidajen malamai a garuruwan Maiduguri Mafa da kuma Banki.
Kwamishinan ya ce gwamnan ya bayar da umarnin gina bandakuna guda 458 a makarantun Firamare da 350 a fadin Jihar.
Gwamna Zulum bayan kammala da bude makarantar da yayi ya bayar da izinin gina gidaje 200 domin sanya ‘yan gudun hijira a ciki da ke kauyen Miringa a karamar hukumar ta Biu ta jihar.