Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kama wani Likita da ta ke zargin ya na da hannu wajen hallaka wasu marasa lafiya tare da sace motocinsu.

Rundunar ta bayyana cewa Likitan mai suna Abbas Adeyemi mai shekara 36 ya na yiwa marasa lafiya allurar guba bayan sun mutu ya sace motocinsu.

Jami’an sun tabbatar da cewa likitan ya na aiki ne a wani babban Asibiti da ke Jihar Kwara.

Bayan kama likitan ya shaidawa jami’an ‘yan sandan cewa ya sace motocin wasu marasa lafiya biyu wadanda ya yi musu allurar guba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ta Edo Chidi Nwabuzor shine ya tabbatar da hakan a jiya Talata.

Kakakin ya bayyana cewa likitan mazaunin garin Offa ne da ke Jihar Kwara.

Chidi ya ce likitan ya kashe wani direban mota mai suna Emmanuel Yobo dan shekara 39 a farko watan Satumba bayan ya yi masa allurar guba.

Kakakin ya kara da cewa likitan ya shaida musu cewa bayan direban ya mutu yaje ya jefar da gawarsa daga bisani kuma ya sace motarsa.

Chidi ya ce a yayin binciken da jami’an tsaron su ka gudanar sun gano cewa likitan ya sayar da motar a garin Osogbo.

Bayan kama motar da ya sayarwa da wani mutumi jami’an su ka kamo likitan sannan kuma mutumin ya bayyana wa jami’an cewa ya taba siyan wata mota a gurin likitan bayan ya kashe wani mutumin a Kwara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: