Ministan ilmi a Najeriya Mallam Adamu Adamu, ya nuna damuwarsa a kan tarin matsalolin da ma’aikatarsa ke fuskanta.

Ministan ya bayyana cewa ya gagara shawo kan tulin matsalolin da ake fama da su a bangaren ilmi.
A tarihin Najeriya, babu wanda ya dade a kan kujerar Ministan ilmi irin Adamu Adamu, tun a watan Nuwamban 2015 aka rantsar da shi.

Dadewar da Ministan ya yi yana jagorantar bangaren ilmi, bai kawo cigaban da aka yi tunani ba.

Mallam Adamu Adamu yace a lokacinsa ne adadin yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya suka kara yawa, a maimakon adadin ya ragu.
Bugu da kari, Ministan yace bai iya kawo mafita a kan yadda za a shawo karshen yajin-aikin da malaman jami’a ke yawan yi a Najeriya ba.
Karatun gaba da sakandare yana fama da kalubale iri-iri a kasar, Ministan ilmin ya yarda cewa bai yi nasarar magance wadannan matsaloli ba.