Wata gobara ta yi kaca-kaca da dakuna 14 na wata makaranta mai suna Tsangya Model Boarding Primary School a yankin Kanwa ta karamar hukumar Madobi a jihar Kano.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), Dr Saleh Jili ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya kawo kayan rage radadi ga makarantar.

Ya ce sun zo ne a madadin gwamna Abdullahi Ganduje domin jajantawa makatantar da kuma ba da tallafin rage radadi tare da fatan hakan zai rage radadin garesu.

Jili ya bayyana cewa, daga kayayyakin da gwamnati ta bayar akwai buhunna 20 na masara, 20 na shinkafa, 2 na Maggi, man gyada, bargo 212 da kuma gidan saura 212. Sauran kayayyakin sun hada da tabarmai, bokitin roba, farantin cin abinci, kofuna da cokala.

Ya bukaci jama’ar gari, musamman mata masu amfani da murhun itace, gas da gawayi su kula kuma ake kashe kayayyakin wutar lantarki duk lokacin da ba a amfani dasu.

A nasa bangaren, shugaban hukumar makarantun Islamiyya da Tsangaya a jihar Kano, Gwani Yahuza Danzarga ya yaba wa gwamna Ganduje da hukumar NEMA bisa wannan halin kirki da sukayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: