Gwamnatin tarayya za ta soma biyan bashin albashin watanni takwas da suka taru ga malaman jami’an da suka yi yajin-aiki a shekarar nan.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a yammacin Lahadi, 6 ga watan Nuwamba 2022, tace ‘yan kungiyar nan ta CONUA ne kurum aka ware za a biya kudin.
Kungiyar CONUA ta bangare ne daga ASUU, wanda ta jagoranci dogon yajin-aikin da aka yi.

Wani ‘dan kungiyar CONUA da ke karantarwa a jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife, ya shaidawa jaridar cewa Chris Ngige ya nuna zai biya su kudin da suke bi.

Malamin jami’ar yake fada a ranar Lahadin nan cewa Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, ya kyankasa masu cewa za a biya su albashinsu.
A cewar wannan malami da ya yi hira da manema labarai ba tare da ya bari an dauki sunansa ba, Minista ya fada masu su sa ran shigowar kudinsu a yau Litinin.
Majiyar ta shaida cewa Ministan ya yi alkawari zai magance matsalar rabin albashin da aka biya malaman jami’a, amma wannan ba zai shafi ‘Ya ‘yan ASUU ba.