An gurfanar da wani matashi dan shekara 25, Abubakar Muhammad, yau Alhamis a kotun Shari’a dake Magajin Gari, jihar Kaduna kan laifin satar Burodi.

Baya ga Satar Burodin, an tuhumcesa da laifin dabawa mai sayar da da Burodin, Isah Hamza, wuka.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Abubakar da farko ya musanta tuhumar da ake masa kuma aka bashi beli.

Alkalin ya bada sharadin cewa ya samu wani ya tsaya masa kafin a sake shi.

Bayan kwashe kwanaki 45 a gidan yari, Abubakar ya sauya jawabinsa inda ya amince da cewa lallai ya aikata laifin.

Mai Burodin ya kashe N56,000 don jinyar raunin da yaji masa.

Daga bisani Alkalin, Malam Rilwanu Kyaudai, ya saki mai laifin bisa azabar kwanakin da ya kwashe a garkame kuma ya umurcesa ya biya N5,000 kudin jinyar mai buredin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: