Al’ummar kauyen Hayin gado da ke cikin karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja sun shiga tashin hankali sakamakon garkuwa da aka yi da ‘ya’yansu fiye da sati uku da su ka gabata.

Kauyen da ‘yan bindigan su ka yi aika-aikar da ke cikin karamar hukumar Rafin yana kan iyaka ne da karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar ta Kaduna wanda ‘yan bindigan su ka addaba da kai hare-hare.

Shugaban matasan yankin na hayin gado Malam Auwal Barau ya ce tun bayan garkuwa da aka yi da ‘ya’yan nasu mutanen yankin sun tsere sun bar gidajen su.

Malam Auwal ya kara da cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da yaran ne a lokacin da su ka tafi gona dibar gyada.

Shugaban ya ce tun bayan yin garkuwa da yaran da su ka kasance su 16 da maza hudu dukkan su kuma masu kananan shekaru ne kuma har yanzu babu wani cikakken bayani akansu.

Malam Auwal ya kuma yi kira ga mahukunta da su taimaka su sanya hannu domin a sako musu ‘ya’yannasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: