Da yawan mutane za su so sanin dalilin buɗe kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Najeriya, tare da ayyukan da suke yi don ga,ar da al’umma.

NAN dai shi ne kamfanin dillancin labarai na ƙasa wanda gwamnatin tarayya ta ƙirƙira da nufin rarraba labarai ga kafafen yaɗalabaran ƙasar da ƙasashen ƙetare.
An samar da kamfanin ne fiye shekaru masu yawa tun bayan da aka bawa Najeriya ƴanci.

Mun sami damar ganawa da Jagora a Kamfani dillancin labarai na ƙasa reshen jihar kano Tukur Muntari Masanawa wanda ya bayyana kamfanin a matsayin sha kundum ganin yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ma ƙasashen ƙetare ke bibiyarsu don samun labarai a sassa daban daban.

Masanawa ya ce ma’anar NAN shi ne News Agency of Nigeria da hausa kuma ana kiransa kamfanin dillancin labarai na ƙasa saɓanin wasu da suke tunanin ko kamfanin madara ne.
“Kusan dukkanin kafafen yaɗa labaran da suke a ƙasar nan ba wanda basu da alaƙar aiki da mu, sannan akwai wani kuɗi da suke biya wanda da zarar sun buɗe shafinmu za su samu labarai sahihai a kowanne fanni” Masanawa.
Sannan akwai tsari da suke da ƙasashen ƙetare na ban gishiri in baka manda wanda har ƙasar Sin wato China ma sukan ɗauki labarai daga garemu.” Inji masanawa.
Ya cigaba da cewa idan mutum na so labarinsa ya yaɗu ko ina a jaridu da gidajen rediyo da ma na TV matuƙar yayi magana da su tamkar yayi magana da kowa ne, kamfanin dillancin labarai na ƙasa dai na nan a kan titin France Road lamba 1B domin ƙarin bayani za ku iya kiran lamba 08077851293.