Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Bankin zai kirkiro wasu sabbin kudade a Kasar da su ka hada da 2,000 5,000 da kuma dubu 1,0000.

Daraktan Kudi na Bankin Ahmad Bello Umar ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da Muryar Amruka a ranar Litinin.

Daraktan ya ce dukkan jita-jitar da ake yadawa na kirkiro wasu sabbin kudaden ba gaskiya ba ne.

Ahmad Bello ya kara da cewa a halin yanzu babu wani babban kudi a Najeriya da ya wuce naira dubu 1,000.

Daraktan ya kuma yi bayani dangane da cire rubutun Ajami a jikin kudin ya ce baza a cire rubutun Ajami daga jikin kudin ba.

Daga bisani kuma ya ja hankulan al’umma da su guji karbar kudaden da su ka haura daga naira 1000 a dunkule.

Ya ce dukkan wanda aka kama da bayar da wadannan kudade a mika ga hukumomi domin yi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: