Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka wani tsohon kwamishina Cif Gab Onuzulike da wasu mutane biyar a Jihar Enugu.

Lamarin ya faru ne a ranar juma’a a karamar hukumar Oji River a Jihar a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta dawowa daga gurin jana’iza.
A yayin isowar kwamishinan ‘yan bindigan su ka hallaka dan uwan nashi sannan su ka yi awon gaba da Onuzulike da motar sa daga bisani shi ma su ka hallaka shi.

Wani rohoto daga rundunar ‘yan sandan Jihar ya bayyana cewa jami’an ‘yan sandan sun hallaka biyu daga cikin ‘yan bindigan tare da kwato motar kwamishinan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kafin kashe kwamishinan ‘yan bindigan sun hallaka wasu mutane biyu a Aguikpah da ke karamar hukumar Nkanu East a Jihar a ranar Juma’a.
Kafin hallaka Tsohon kwamishinan ya kuma rike mikam tsohon shugaban karamar hukumar ta Oji River ta Jihar.