Rundunar yan sandan jihar Ogun tabbatar da kama wani mutum da ake zarginsa da dukan matarsa wanda ya kai ga ta rasa ranta.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ogun shi ne ya bayyana haka a shafin rundunar na twitter.
Wanda ake zargin mai suna Segun Omotosho ana zargin sun sami sabani da matarsa sakamakon ta ki sanya sunansa a wata makarantar Framare da ta gina ta saka wanda hakan ya jawo musu musayar yawu inda ya kai ga dukanta har ta mutu.

Wani shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce matar ta turawa yan uwan ta sakon murya inda take cewa mijinta na dukanta kuma inta mutu shi ne.

Sannan ya ce mijin ya yi amfani da mukalli tare da buga mata akai a yayin dukan nata kuwa ta rasu.
Rundunar ta ce ta samu nasarar kama wanda ake zargin bayan yayi kokarin tserewa kuma ana ci gaba da bincike kafin daga bisani a gurfanar da shi a gaban kotu.