Wasu tsaregun ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu garuruwan Zamfara inda suka yi garkuwa da mutum fiye da 100 da suka hada da mata da yara.

An tattaro cewa maharan sun kai hari garuruwa da dama ciki harda kauyen Kanwa a karamar hukumar Zurmi ta jihar a ranar Lahadi.
Kwamishinan labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, da mazauna garuruwan sun tabbatar a ranar Litinin cewar an sace mutum fiye da 40 a kauyen Kanwa.

Hakazalika, wani mazaunin garin Kwabre a karamar hukumar ta Zurmi ya bayyana cewa an sace akalla mutum 37 wadanda yawancinsu mata da yara ne.

Wani mazaunin kauyen ya ce Yanzu haka, kauyen Kanwa ya zama kamar kufai, ‘yan bindigar sun raba kansu gida biyu sannan suka farmaki garin, sun yi awon gaba da yara tsakanin shekaru 14 zuwa 16 da kuma mata.
An kuma tattaro cewa a garuruwan Yankaba da Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun, an sace akalla mutum 38 yayin da suke hanyarsu ta zuwa aiki a gonakinsu.
Da yake korafi kan lamarin, VOA ta rahoto cewa kwamishinan labaran ya yi ikirarin cewa yan ta’addan na amfani da wadanda suka sace a matsayin kariya daga hare-haren rundunar sojojin Najeriya.