Wata kotun daukaka kara mai zamanta a jihar Sakkwato ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar game da soke zaben fidda gwanin gwamna da aka gudanar a jihar Zamfara.

Mai sharia  Shuaibu Muhammad ya ce daukaka karar da jamiyyar  PDP ta yi bai da makama don haka ilahirin alkalan kotun sun amince da tabbatar da hukuncin baya.

Sannan alkalin ya yi Karin haske da cewa , dan takarar jam’iyyar PDP Lawal Dauda Dare bai da hurumin daukaka kara kan hukuncin da a baya ya amince da shi.

Haka zalika, kotun ta umarci jam’iyyar PDP ta biya tarar naira 100,000 bisa bata lokacin kotu.

Tun da farko dan takarar gwamna na jamiyyar PDP, Ibrahim Shehu ya kalubalanci abokin takarar ta sa Lawal Dare a nasarar da yayi a zaben fidda gwani na gwamna a jihar ta Zamfara.

Shehu na zargin an yi murdiya a zaben fidda gwanin tare da saba kaidojin zabe wanda  INEC ta shar’anta.

Sai dai ganin bai gamsu da zaben ba, ya tunkari kotun tarayya mai zamanta a Gusau, kuma ta rusa zaben tare da ba da umarnin a sake shi cikin kwanaki 14.

Leave a Reply

%d bloggers like this: