Gwmnan jihar Gombe Mahammad Inuwa Yahaya bayyana cewa al’umma su zuba hannun jari a sabuwar rijiyar man fetur din da za’a hako a jihar.

Mahammad Inuwa ya bayyana haka ne a cikin wata hira da suka yi da tashar Talabijin ta BBC.

Ya ce dole jama’a su kwantar da hakalin su so zo a ci moriyar lamarin gabaki daya.

Ya ci gaba da cewa wannan aiki da za a yi na hakar man fetur da kuma wasu kamfanunuwan hada taki wanda wasu mutane ne su ka sanya kudaden su daga kasar indiya tare da taimakon gwamantin tarayya.

Kuuma jama a ba su riki abun hannu biyu-biyu ba to nan gaba ma ba za a samu wadanda za su so su yi bincike ba kuma su gano tun da abun a jihar su ya ke amma ba su da ilimin sanin hakan .

Sannan ya ce ko shugaban kasa Mahammadu Buhari sai da ya basu shawarwari inda ya ce su zauna lafiya domin akwai arziki a lamarin man fetur.

A cikin da makon da mu ke  bankwana da shi ne shugaban kasa Mahammadu Buhari ya je jihar Gombe domin fara aikin wata rijiyar man fetur da aka gano a jihar ta farko a Arewacin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: