Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano wasu mutane 100 da su ke turawa yan kunguyar taaddanci kudade a fadin kasar.

Yayin da yake magana a wajen taron mai taken ba kudi ga dan ta’adda babban ministan harkokin ciki gida Rauf Arebesola ya bayyana haka ta bakin mai taimaka masa Abdulmalik Sulaiman a jiya Lahadi.
Rauf ya ce bayan binciken watanni 19 da suka gudanar sun samu nasarar kama mutane 100 wadanda suke taimakawa Yan ta’adda da kudade.

Ya ci gaba da cewa sun yi amfani da hukumar NFIU tare da takwarorinta na tsaro wajen gudanar da binciken.

Sannan ya ce mutanen 100 da suka gano sun fito ne daga kasashe Goma na duniiya.
Sannan ya ce sun kama mutane 48 daga ciki bayan shafe watanni ana binciken.
Sannan daga karshe minista Rauf Arebesola yayi kira ga gwamnati data kara walwalar mutane dalibai da kuma masu neman aikin yi domin dakile matsalar rashin tsaro a fadin kasa Najeriya.