Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara hadin gwiwa da jami’an sa-kai ta tabbatar da kubtar da mutane 15 da aka yi garkuwa da su,tare da kama ‘yan bindiga bakwai a Jihar.

Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Yusuf Koli ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake holan batagari ga manema a ranar Alhamis.
Koli ya bayyana cewa an samu nasarar kubtar da mutanen ne a ranar Litinin bayan kwashe kwanaki 50 da su ka yi a hannun ‘yan bindigan.

A yayi holan kwamishinan ya ce rundunar ba za ta gajiya ba wajen ganin an tabbatar da ingantaccen tsaro a cikin Jihar.

A cikin wata takarda da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Muhammad Shehu ya ce daga cikin ‘yan ta’addan da aka kamo ana zargin mutane shida da laifin tsoratar wa da kuma karbar kudade daga mazauna kauyukan Jihar.
Shehu ya kara da cewa kudin da aka samu a hannun ‘yan bindigan sun kai naira 700,000 wanda su ka karba daga mazauna kauyukan kananan hukumomin Anka a matsayin kudin haraji.
Kakakin ya ce jami’an sun kuma kama wata mata wadda ake zargin ta da samar wa ‘yan bindigan makamai a Jihar.
Kazalika Shehu ya ce matar ta kware wajen samar wa da batagarin makamai wanda ta ke yin safarar sa.
Muhammad Shehu ya bayyana cewa bayan kubtar da mutanen sun mika su ga Asibiti domin kula da lafiyar.