Gwamnonin jihohi 36 da ke fadin Najeriya sun yi wa Gwamnatin Tarayya raddi kan jefa ’yan Najeriya cikin talauci da matsin rayuwa.

Kungiyoyin Gwamnonin Najeriya (NGF) ta ce babu abin da ya jefa ’yan Najeriya cikin talauci da matsin rayuwa in banda gazawar Gwamnatin Shugaba Buhari wajen cika kangin talauci.
Kakakin kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya ce, a lokacin yakin neman zaben 2019 Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga talauci, amma yanzu ’yan kasar miliyan 130 sun talauce.

Martanin kungiyar na zuwa ne bayan Minista a Ma’aikatar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Clement Agba, ya dora wa gwamnoni laifin karuwar talauci a Najeriya, inda mutum bakwai cikin kowane ’yan kasar 10 ke cikin talauci.

Ministan ya zargi gwamnoni da fifita gina filayen jirgin sama da gadojin sama, maimakon mayar da hankali wajen fitar da ’yan kasa mazauna yankunan karkara daga talauci.
Washegari kuma Shugaban Kasa
gwamnoni da wawushe kudaden da ke tura wa kananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya.
Sai dai kakakin kungiyar gwamnonin, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya ce bai kamata Gwamnatin Tarayya ta zarge su ba,
alhali a gwamnati mai ci da Mista Clement Agba yake minista, kamfanin NNPC, wanda shi ne babbar kafar samun kudaden gwamnati ya gaza ba da kudaden da za a tura a jihohi na tsawon watanni.
Ya ce, abin da ya kamata shi ne Mista Clement da takwararsa, Zainab Ahmed su fito su yi bayani, me ma’aikatarsu ke yi domin fitar da ’yan Najeriya daga talauci.