Gwamnatin tarayya ta raba Kayan Sarrafa madarar shanu a jihar Kano karkashin ma’aikatar aikin gona da raya karkara, ta raba sabbin motocin raba madarar shanu mai na’urorin sanyi, guda 100 ga kungiyar masu sayar da madarar, da ke jihar Kano.

Darakta a ma’aikatar aikin noma da raya karkara da ke jihar Kano, Alhaji Baba Gana ne ya mika kayan ga kungiyar a madadin ma’aikatar.
Alhaji Gana ya ce, sauran kayan da aka raba wa kungiyar sun hada da janareta mai karfin 20KBA.

Gana ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin na raba kayan domin tabbatar da kara tsaftace kasuwancin na madara a jihar da kuma a kasa baki daya, A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi namijin kokari wajen ganin ana kara bunkasa fannin na sarrafa madara a kasar nan.

Alhaji Gana ya ci gaba da cewa, an kuma gina cibiyoyi biyu na tara madarar shanu, inda aka mika su ga kungiyar.
Daraktan ya bayyana cewa, an kuma horas da wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar kan fanni daban-daban na hada-hadar kasuwancin madarar ta shanu.
Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bunkasa fannin na sarrafa madarar shanu, har sai kwaliyya ta biya kudin sabulu, musamman domin a samar da wadacacciyar madarar shanu a kasar nan.
Da yake karbar kayan tallafin, shugaban kungiyar reshen jihar Malam Usman Abdullahi ya jinjinawa ma’aikatar bisa talafin da aka baii wa kungiyar.
Malam Usman ya kuma bayar da tabbacin cewa, kungiyar za ta yi amfani da Kayan yadda ya dace.