Wasu yan bindinga sun sace wani basaraken Fulani mai suna Alhaji Aliyu Abdullahi a kauyen Maganda da ke karamar hukumar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Basaraken wanda ake kira da Ardon Makera, an sace shi ne  a yammacin ranar Litinin misalign karfe 6:12 a kauyen Janjala, akan hanyarsa ta dawowa kauyen Maganda.

Ardon Makera dai shi ne shugaban Fulanin karamar hukumar ta Kagarko, kuma alamarin ya rutsa da shi ne yayin da yake dawowa daga wani taro na masu rike da sarautun gargajiya kan hare haren da aka kai wa kauyukansu a yan kwanakin nan.

Hakan na zuwa ne kasa da kwana shida bayan da wasu yan bindiga su ka kai hari tare da sace mutane 37 ba kauyukan jihar ta Kaduna.

Har zuwa wannan lokaci dai rundunar yan sanda ba ta ce komai ba kan alamarin

Leave a Reply

%d bloggers like this: