Gwamnatin jihar Kano ta shiya aurar da zawarawa 1,500 a ranar Lahadi 5/5/2019.

Cikin shirin gwamnatin na rage yawan zawarawa a jihar Kano ta shiya aurar da zawarawan tare da basu kayan ɗaki da kuma sabbin shaddoji da angwaye da amare za su saka.
Sama da naira miliyan 30 za a kashe wajen gudanar da bukukuwan.

Gwamnatin ta ce za ta bayar da kuɗin da auka kai naira 20,000 ga kowanne ango bayan kuɗin sadaki da za ta biyawa kowannensu.

Za a yi aurrn ne a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin Kano bayan an yi gwaje gwajen jini da wasu nau ikan cuta.
Mujallar Matashiya ta gano cewa mafi yawa daga cikin auren da ake yi ana samun matsalolin da auka shafi cuta, wasu ma suna da aure su zo a kuma ɗaura musu, kar yadda a wasu lokutan adadin da gwamnatin ta ke faɗa baya kaiwa, ko saboda tagomashin da aka warewa kowanne ma auratane, a wannan karon dai za mu zuba ido mu gani don ganin matakin da za a ɗauka.