Hukumar Hisbah a jihar Kano ta bayyana cewa, ta lalata kimanin manyan motoci dauke da giya guda 25 daga farkon watan Janairun wannan shekarar zuwa yanzu.

Sannan kuma ta kama mutane masu aikata manyan laifuka, wadanda suka kai adadin mutane 2,260 a cikin ayyukan da tayi a shekarar nan da take shirin Karewa.

Babban kwamandan rundunar ta Hisbah Sheikh Harun Ibn Sina shi ya bayyana hakan, a jiya Alhamis yayin wata tattaunawa da manema labarai a Shalkwatar hukumar a jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa, manyan motocin suna dauke da dubunnan mabanbantan kwalaben giya. Kuma yace zasu kuma fasa wasu kwalaben kafin watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa.

Sannan yace wadanda aka kama da laifuka kuma an damka su a hannun hukumomin tsaron da abin ya shafa, sannan masu karancin shekarun cikinsu kuma an damka su hannun iyayensu.

Ibn Sina ya kara da cewa, sun sulhunta rigingimu kimanin 822. Sannan kuma wasu rikice-rikicen suna gaban mabanbantan kotuna sakamon rudanin da yake cikinsu.

A karshe ya bayyana cewa, sun aurar da ma’aurata 15 a hukumar. Sannan mutane 22 sun karbi Addinin Musulunci a lokutan Da’awah a sassan Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: