Gamayyar kungiyoyin matasan arewa mazauna Legas sun bayyana cewa lallai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya saurari koke-koken al’ummar kasar nan wajen kara yawan adadin kudaden da za a dunga cirewa a duk kullum.

A baya dai, CBN ya kakaba dokar kayyade cire kudade wanda a duk kulum mutum zai iya cire naira 20,000, yayin da a mako mutum zai iya cire naira 100,000 kacal.
Sai dai daga baya CBN ya kara yawan kudaden ya tashi daga naira 100,000 zuwa naira 500,000 a duk mako.

Inda kamfanoni za su iya cire naira miliyan 5 maimakon dubu dari biyar a mako. Dokar kayyade kudaden za ta fara aiki ne tun daga ranar 9 ga watan Janairun 2023.

Mafi yawancin al’ummar Nijeriya sun nuna gamsuwarsu game da wannan mataki da CBN ya dauka na kara yawan kudaden, wanda suke ganin cewa lallai CBN ya saurari koke-koken al’ummar kasar nan.
Ya ce, a matsayinsa na wadanda suke mu’amala da al’umma suna ganin sauya wannan salo da CBN ya sauya ya ji kiran talakawa. Ma’ana gwamnati ta sausauta wa marasa karfi.
Shugaban gamayyar, Alhaji Ibrahim Galadanci ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.