Gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye karin albashin da ta ce za ta yiwa ma’aikata da kuma jami’an gwamnatin a shekarar 2023 mai kamawa.

Mai magana da yawun ma’aikatar Kwadago da samar da ayyukan yi Mista Olajide Oshundun shine wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Kakakin ya ce gwamnatin ba ta yin aiki akan albashin ma’aikata ta inda ya ce gwamnatin na yin duba ne kawai akan a wasu alawus.

Olajude ya kara da cewa wasu alawus-alawus ne kawai na musamman ne kawai gwamnatin ta ke shirye-shiryen kara ma’aikatan.

Mista Olajide ya bayyana cewa tuni aka mikawa kwamitin Albashi na fadar shugaban kasa wanda zai yi duba akan karin alawus din wasu ma’aikata da hukumomin gwamnati ta hannun Sakataren gwamnatin tarayya.
Kakakin ya ce karin zai ragewa ma’aikata radadin hauhawar farashi kayayyakin abinci.
Kazalika Oshundun ya ce matukar za ayi karin albashi sai an tattauna da kungiyoyin kwadago a matsayin wakilan ma’aikata.