Kungiyar fulani makiyaya ta Miyatti Allah MACBAN ta bayyana cewa babu wani dan takara shugaban kasa da ta ke goyan baya a yayin zaben shekarar 2023.

Shugaban Kasa kungiyar na kasa Alhaji Baba Usman-Ngelzarma ne tabbatar da hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.
Baba Usman ya ce dukkan manyan jam’iyyun siyasar Najeriya ba su sanya manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta ba a yayin bayyana manufofin bayan sun ci zabe.

Ngelzarma ya ce don haka babu wata jam’iyya da za su goyi bayan ta a yayin zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Shugaban ya kara da cewa kungiyoyin fulani sun kasu kashi biyu da Kungiyar miyatti Allah kautal hole da kuma miyatti Allah MACBAN idan ya ce kungiyar ba ta goyan bayan kowanne dan takara.