Wata gobata ta kone wasu gine-gine biyu wadanda ke dauke da gadaje akalla 40 da ke garin Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.

Rahotanni daga Jihar sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne a safyar ranar Juma’a a kewayen Titin Boms da ke unguwar Elekahia.

Daya daga cikin ginin da gobarar ta kone na dauke da ginin bulo yayin da dayan ya kasance ginin katako.

Rahotan ya bayyana cewa ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon tukunciyar gas.

A yayin tashin gobarar ta cinye dukiya mai tarin yawa wanda hakan ya kawo cikas ga jami’an kashe gobara kafin su kashe ta.

Bayan kashe gobarar hukumomi a Jihar ba su iya gano a dadin asarar da aka tafka a yayin gobarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: