Shugaban kasa Muhammad Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2023 mai kamawa.

Shugaban zai sanya hannun ne a ranar Talata 3 ga watan sabuwar shekarar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmad bayan kammala tattaunawar da shugaba Buhari a fadar sa dake Abuja a jiya Juma’a.

Ahmad lawan wanda ya halarci zaman majalisar da misalin karfe uku na yamma tare da shaida musu yadda tattaunawar ta kasance.

Shugaban majalisar tattaunawar ta su ta sake yin duba akan bukatar karin aron kudi tare da maganar kasafin kudin shekarar 2023.
Lawan ya ce shugaban ya bayyana masa cewa zai sanya hannu akan kasafin kudin.