Hukumar Hisbah a jihar Kano ta tabbatar da sahihancin auren matar da akr zargi ta kashe aurenta ta auri saurayin ƴarta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim Fagge ya sanyawa hannu a yau, y ace hukumar ta gamsu da sahihancin auren matar da mijinta.

Tun da farko labarai sun yi ta yawo a kafafen yada labarai cewar, wata mata a ƙaramar hukumar Rano ta kashe aurenta tare da aure saurayin ƴarta.

Shugaban kwamitin da hukumar ta kafa domin bi9ncike a kai, ya gabatar da rahotonsa, kuma hukumar ta gamsu da sahihancin auren bisa wasu hujjoji  guda biyu ƙwarara da ya gano.

Sai dai hukumar ta tabbatar da cewar bazawarin da matar ta aura ya taɓa neman auren ƴarta a baya amma hakan bai yuwu ba.

Kwamandan hukumar Hisbah Ustaz Haroon Ibn Sina ya yabawa kwamitin tare da ƙarfafarsu don cigaba da jajircewa a kan ayyukan da su key i yau da kullum.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: