Gwamnan bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya amsa gayyatar da majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta yi masa domin bayani a dngane da sabbin kuɗi da aka sauyawa fasali.

Kwamitin wanda shugaban masu rinjaye a majalisar Alasan Ado Doguwa ya ke jagoranta, ya buƙaci haɗin kan babban bankin da bankunan ƴan kasuwa a cikin tsarin.
Tun a baya kwamitin ya gayyaci gwamnan bankin amma ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa.

Halartar da gwamnan bakin yay i na zuwa ne bayan da aka tsawaita lokacin daina karɓar tsofaffin kuɗin da aka sauya zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu mai kamawa.

Gwamnan ya bayar da uzirin rashin halartar gayyatar da aka masa a baya kasancewar ya ziyarci ƙasar Senegal don gudanar da wani aiki.
Godwin Emefiele ya tabbatar da cewar bankuna za su ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi bayan wa’adin da aka ƙara na 10 ga watan Fabrairu mai kamawa.