Chiza Dani waƙa ce da ke tashe a kafofin sadarwar zamani wadda matasa maza da mata ke sauraro a kwanakin nan.

Mawaƙi Abdul D. One ya bayyana mana ma’anar kalmar a wata tattaunawa da Mujallar Matashiya.
Ya ce kalmar ya arota ne daga harshen Buzanci yayin da ya yi wata tafiya zuwa jamhuriyar Nijar.

Abdul D. One ya ce tun bayan da ya ga kalmar rubuce a wayar wani abokinsa a Agadez daga wannna lokacin ya dinga bi har sai da ya gano ma’anar waƙar.

A tattaunawar ya tabbatarwa da Mujallar Matashiya cewar bayan gano ma’anar kalmar ashe ta na nufin ‘Daɗina’ wato kalmar masoyi ko masoyiya a harshen Buzanci.
Ya ce kalmar ta yi daidai da sunan soyayya da ake faɗawa masoya mace ko namiji.
A halin yanzu ana shirin ɗaukar bidiyon waƙar da za a fitar da shi ba da daɗewa ba.
Sai dai ya ce babu fim da ake yi a kan waƙar bai sani ba ko nan gaba.
Mawaƙi Abdul D. One wanda waƙoƙinsa ba su fi hamsin ba a cewarsa.
Sai da ya ce a waƙoƙinsa ba wadda ya fi so kamar waƙar Mahaifiya.
Sai wasu kamar Kar Ki Manta Da Ni, Chiza Dani, Ina Sonki da sauransu.