Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya, Chris Ngige ya ce an kammala duk wasu shirye-shirye na karin albashin ma’aikata.

Rahoton da Daily Trust ta wallafa a yau Laraba cewa Chris Ngige ya shaidawa jama’a, gwamnatin tarayya za ta fito da sabon tsari na biyan ma’aikata.

Ministan ya ce za ayi hakan ne nan da watan Mayun shekarar 2024 ko kafin zuwa lokacin.

Dr. Chris Ngige ya kuma ja kunnen kungiyoyin ‘yan kwadago da su guji yi wa gwamnati katsalandan, su na neman tursasa abin da suke so ayi.

Ya yi wannan jawabi ne yayin da aka gayyace shi zuwa wajen taron kungiyar ‘yan kwadago ta kasa NLC a birnin tarayya Abuja.

A wajen taron da aka yi ranar Talata ne Ministan tarayyar ya gargadi mahalartan cewa su na sabawa dokar kwadago da ta wajabta kwas a MINILS.

Tsohon Gwamnan na Anambra yake cewa kafin mutum ya zama shugaba a kungiyoyin kwadago yanzu, sai ya yi kwas a wannan makaranta.

Rahoton ya ce yin karatun zai taimakawa shugabannin wajen fahimtar tsarin aiki.

A jawabin da ya gabatar, Ngige ya yi kira ga kungiyar NLC da ta tabbatar da cewa Gwamnonin jihohin kasar nan sun dabbaka dokar ECA ta shekarar 2010.

Wannan doka ta ba ma’aikata damar samun diyya yayin da suka samu rauni ko suka mutu a wurin aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: