Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za a ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi da aka sauyawa fasali har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu da mu ke ciki.

Hakan ya biyo baayan zaman da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi da majalisar ƙoli ta ƙasa kan sauya fasalin sabbin kuɗin.
Shugabna ya ce gwamnatin za ta mutunta umarnin kotun na tsawaaita lokacin zuwa ranar 15 ga wata.

Kotun ƙoli ta ƙasa ce ta dakatar da gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya CBN daga haramta karɓar tsofaffin kuɗi da aka sauya.

Gwamnoni a Najeriya na ci gaba da sukar lamarin yayin da wasu ke ci gaba da shigar da ƙara gaban kotu bisa ƙin amincewa da matakin.
Tun d afrko gwamnatin tarayya ta baayar da watanni aƙalla huɗu domin sauya tsaffin kuɗin da aka sauya.
Sai dai wasu da dama na kokawa a kan hakanan sanadin ƙarancin sabbin daa aka sauya a hannun jama’a.
A makon da ya gabata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha alwaashin magance matsalar ƙarancin sabbin kuɗi a hannun jama’a cikin mako guda.