Sultan din Sokoto kuma shugaban zauren koli na harkokin Addinin Musulunci Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa, batun sauyin kudi ya kawo yunwa da kuma bacin rai a cikin a kasar nan.

A jiya Litinin ya bayyana cewa, ya kamaga shugaba Muhammadu Buhari ya yi duba na tsanaki Dan shawo kan matsalar. Ya kuma kara da cewa, matsalar rashin kudin ta jefa Al’umma cikin kuncin rayuwa.

A wani taron kwanaki biyu a kan shawo kan matsalar da take addabar kiwon dabbobi da Gwmnatin Kano ta shirya a Abuja, yace akwai karin halin matsi da kudirin canjin kudi na babban bankin Najeriya CBN ya kawo.

Yace idan aka ajiye batun siyasa a gefe, batun cigaba musamman ga talakawan kasar nan shi ya kamata a fara bawa fifiko. Wadannan mutanen da Allah ya Baku shugabancin su. Allah ya kiyaye Amman wata ran zasu taso su yake ku.

Ya kuma bayyana cewa bayan zantukan turanci da farfesoshi suka zayyano, ta yaya za’a kai cigaban ga talakan da yake manomi, Fulanin da basu san komai na cigaba ba? Su kawai dabbobi suka sani a rayuwarsu.

A karshe yace mutane suna cikin yunwa, shin akwai kudin? Ana cikin yunwa da bakin ciki. Ya kamata a duba yiwuwar an kawar da wannan matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: