A yau Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya.

Buhari ya isa bayan mintuna 40 kamar yadda ya saba, yayin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fito fili.

Ministocin da suka halarci taron sun hada da na lafiya, Osagie Ehanire, ministar ayyukan Jin kai da tausayin al’umma Sadiya Farouk, ministan ma’adinai Olamilekan Adegbite, ministan ayyuka, Chris Ngige.

Sauran wadan da suka halarta sun hada da ministan ayyuka da gidaje Babatunde fashola, babban lauyan Najeriya Abubakar Malami SAN, ministan zirga zirgar jiragen kasa Mu’azu Sambo, ministan muhalli Muhammad Abdullahi.

Sauran sun hada da ministocin harkokin mata, Paulen Tallen; Harkokin jin kai, karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, Jirgin sama, Hadi Sirika da kuma harkokin ‘yan sanda, MAIGARI Dingyadi.

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, sun halarci taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: