Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yi barazanar rufe duk wani bankin kasuwanci da ke kin karbar tsohon kudi.

Hakan ya biyo bayan rahoton haramta kudin da wasu bankuna, mutane da kuma yan kasuwa biyo bayan karewar wa’adin 10 ga watan Fabrairu da babban bankin kasa ya bayar.
Gwamnan ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da yake jawabi ga yan kasuwa maza da mata a kasuwar Itoku Kampala a Abeokuta, a wajen yakin neman zaben tazarce.

Abiodun, wanda ya yi tir da hukuncin bankunan, ya ce tunda babu sababbin kudin, dole ne bankuna su cigaba da karbar tsoho don saukakawa al’umma.

Ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankali, yana bada tabbacin gwamnatin sa na aiki tukuru don shawo kan lamarin.
A gefe guda, harkokin kasuwanci sun samu nakasu a ranar Talata biyo bayan zanga-zanga da wasu fusatattun mutane suka yi saboda karancin takardun sababbin N200, N500, da kuma N1000 a Sango-Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta Jihar Ogun.
Mazauna yankin da suka dinga zarya zuwa banki amma sun kasa cirar kudin su.
An ruwaito cewa al’ummar sun fusata ne lokacin da aka ki karbar tsofaffin kudin su da suka kai ajiya.