Akalla ‘yan Najeriya 150 ne a jiya Talata aka dawo da su gida Najeriya daga Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tarbe su a filin jirgin saman Murtala Muhammed International dake jihar Legas.

Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM ce ta dauki nauyin dawo da ‘yan gudun hijirar daga Nijar.

Ko’odinetan hukumar NEMA reshen jihar Legas Ibrahim Farinloye wanda ya wakilci babban darakta Alhaji Mustapha Ahmed ya tarbi mutanen da suka dawo tare da sauran hukumomin gwamnati.

Wadanda aka dawo da su sun hada da manya maza 98, yara maza 11 da jarirai maza biyu yayin da akwai manya mata 24, yara mata 13 da jarirai mata biyu.

Sauran hukumomin da suka shiga aikin sun hada da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), NAPTIP, FAAN, ‘Yan sandan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: