Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙara wa’adin Karɓar Naira 200 zuwa kwana sittin a nan gaba.

Shugaban ya bayyana haka yau yayin daa ya ke jawabi a dangane da batun sauya fasalin kuɗi da ƙarewar wa’adinsa.

A jawabinsa, ya amince da ƙara wa’adin ci gaba da karɓar Naira 200 ne kaɗai bayan kokawa da jama’ar ƙasar ke yi kan ƙaramcin sabbin kuɗi.

Wannan ke nuni da cewa wa’adin naira 500, da naira 1,000 ya ƙare illa mutanen da za su iya kaiwa babban bankin ƙasa CBN bayan cika ƙa’idar da ya saka.

A ranar Laraba, kotun ƙoli a Najeriya ta sanya ranar 22 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron ƙarar da wasu gwamnonin ƙasar su ka kai a kan sauyin kuɗin.

Kuma wasu gwamnoni a Najeriya na tilasta karɓar tsaffin kuɗin duk da cewar wa’adin da gwamnatin tarayya ta saka ya cika a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Fiye da kwana 90 gwamnatin ta bayar domin sauya kuɗi a Njaeriya, sai dai wasu da dama na kallon damar ƙara wa’adin cigaba da karɓa a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: