Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su karaya a halin da ake ciki domin akwai sauƙi a gaba.

Muhammadu Buhari wanda ya aike da saƙon faifen bidiyo daga birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, ya tabbatar da cewar halin da ƴan Najeriya ke ciki akwai wahala.

A cikin saƙon da shugaban ya aike, ya buƙaci ƴan ƙasar da su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam”iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya ce Bola Tinubu mutum ne nagartacce wanda ya yi imani da cewar zai ɗora daaga inda ya tsaya.

Muhammadu Buhari ya aike da saƙon mai ɗauke da ban haƙuri ga ƴan ƙasar a bisa halin da su ka tsinci kansu na sauyin fasalin kuɗi.

Mutane na kokawa a dangane da sauyin fasalin takardun kuɗi sanadin ƙarancin sabbin a hannun jama’a.

A makon da ya gabata, shugaban ya yi wa ƴan Najeriya jawabi da yake shaida cewar, za a ci gaba da karɓar naira 200 zuwa watanni biyu a nan gaba, amma an dakatar da karɓar naira 500 da naira 1,000 baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: