Babban bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa ya sake fito da tsohon takardun kuɗi na naira 200 kuma ya raba wa Bankuna domin yan Najeriya su samu ikon ci gaba da hada-hada da su.

Amma rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa babban bankin ya yi gum da bakinsa kan adadin yawan takardun naira 200 da ya sake fitarwa zuwa hannun jama’a.


Mafi yawan takardun naira 200 da CBN ke ikirarin ya fitar da tsofaffi ne da aka taɓa amfani da su kuma da yawansu an karɓe su daga hannun yan Najeriya lokacin shirin musayar kuɗi.
Wani ma’aikacin CBN ya shaida wa jaridar cewa adadin takardun naira N200 da ke yawo a hannun al’umma ya ƙaru bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar a makon da ya gabata.
Mutumin, wanda ya ƙi faɗin sunansa saboda ba shi da hurumin magana kan lamarin, ya ce, sun raba tsoffin da sabbin N200 a ƙarshen makon nan, ya ce rassan CBN a jihohin Najeriya, sun karbi takardun naira a ƙarshen makon nan kuma za su fara rabawa bankunan kasuwanci.
Haka zalika ya jaddada cewa bankuna sun karbi isassun takardun N200 da zasu zuba a na’urar ATM domin su isa hannun mutane.
Sai dai ya ƙi ya bayyana adadin yawan takardun kuɗin da suka baiwa bankuna domin ta haka ne kaɗai za’a iya gane tasirin da zasu yi wajen rage raɗaɗin halin da mutane ke ciki.