Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ƙarancin sababbin kuɗin da ake fama da shi na sanya mutane cikin wahala, inda yake cewa duk da matsayin sa na gwamna, baya da sababbin kuɗin.

Adeleke ya koka kan yadda ƙarancin kuɗin ya sanya mutanen jihar cikin tsaka mai wuya inda yace yana bakin ƙoƙarin sa wajen ganin an yayyafawa fitinar da ka iya ɓallewa ruwa a jihar.


Yace zai tabbatar bankuna da ofishin babban bankin Najeriya (CBN) na jihar sun samu kariya.
Da yake jawabi ga jami’an CBN yau Talata a ofishin sa, Adeleke ya nuna damuwar sa kan ƙarancin sababbin kuɗin, inda yayi kira ga CBN daa su hukunta duk bankunan da ke da hannu wajen azabtar da al’umma.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa a shirye take ta haɗa hannu da CBN domin musayar kuɗin, inda ya gayawa tawagar CBN ɗin cewa jihar na yin bakin ƙokarinta wajen ganin mutane sun kwantar da hankulan su.
Gwamnan ya ce Kwata-kwata babu sababbin takardun kuɗi, duk da yana matsayin gwamna, bashi da sababbin kuɗin, balle talakawan jihar sa.