Wata kotun majistire da ke zaman ta a Jihar Filato ta aike da wani matashi mai shekaru 35 gidan gyaran hali sakamakon zagin mahaifinsa da yayi tare da yi masa barazana.

Kotun ta yanke masa hukuncin zaman shekara daya a gidan gyaran hali bayan amsa laifin sa da yayi.


A yayin yanke hukuncin kotun ta yanke masa zaman watanni shida a gidan gyaran hali tare da zabin biyan tarar naira dubu goma sakamakon zagin mahaifinna sa.
Sannan kotun ta sake yanke masa hukuncin watanni shida a gidan gyaran halin ba tare da zabin biyan tara ba bisa laifin yiwa mahaifinsa barazana.
Wanda ake zargin ya aikata laifin ne tun a ranar 26 ga watan Disamban 2022.
Matashin ya fitar da mahaifin sa daga gidansa tare da zanginsa , sannan ya yi masa barazanar kone gidan mahaifin nasa matukar bai bashi naira dubu dari biyu ba.
Mai shigar da kara ya bayyana cewa laifin da matashin ya aikata ya sabawa sashe na 377 da 379 na kundin final kod na Jihar.
Alkalin kotun ya tabbatar da cewa hukuncin da aka yankewa matashin zai zama jan kunne ga masu shirin aikata hakan a nan gaba.