Jam’iyyar APC mai mulki ce ta ke da rinjaye zuwa yanzu a zabukan majalisar dattawa kamar yadda sakamakon hukumar INEC suka tabbatar.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben majalisar dattawa 38, yayin da jam”iyyar PDP mai hamayya ta yi nasara a kujeru 21 da aka sanar.

 

Jam’iyyar LP da tayi farin jini a zaben 2023 ta samu kujerun Sanatoci hudu, sai jam’iyyar SDP tayi galaba da kujeru biyu a zaben majalisar dattawa.

 

Haka zalika jam’iyyun YPP da NNPP za su samu kujera a majalsar tarayya ta goma da za a rantsar.

 

Rahoton ya ce wadannan su ne kason kujeru 67 da aka sanar a zaben 2023. Sai dai babu tabbacin cewa jam’iyyar APC mai-ci za ta cigaba da rike rinjayenta.

 

Kafin a ce jam’iyya ta samu rinjaye a majalisa, sai ta na da akalla biyu bisa ukun kujeru 109. Kowace jiha ta na da Sanatoci uku, sai Abuja ta na da guda.

 

A cikin sakamakon da aka samu, Sanatoci 18 sun lashe zaben tazarce ne, ragowar sun je ne a karon farko ko kuma sun taba zama ‘yan majalisar wakilai.

 

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Lawan yana cikin wadanda za su koma, amma ba tabbas ba ne shi ne zai cigaba da rike kujerar a yanzu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: