Kungiyar ‘yan kabilar yarabawa zalla ta Afenifere tayi tur da Allah wadai da ayya Asiwaju Bola Ahmad Tunubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan fabrairu da ya gabata.

Afenifere ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta Pa Ayo Adebanjo, a lokacin wata tattauanwa ta wayar tarho da BBC,Adebanjo ya cigaba da bayyana zaben da ya baiwa Tunubu nasara a matsayin zabe dake cike da kura-kurai.
Ya kara da cewa zaben shugaban kasa ba abune da zasu amince dashi ba kana hakan na iya haifar da rikici a kasar a cewarsa.

Adebanjo ya cigaba da cewa gazawar da Hukumar zaben kasar ta yi na amfani da da na’urar BVAS a ruumfunan zabe kamar yadda tayi alkawari tunda fari, ya nuna cewa wasu ne suka tsara yadda zaben zai gudana da kuma dan takarar da suke son ya yi nasara a zaben.

Adebanjo ya kuma bayyana cewa shi dai a iya saninsa ba’ayi zabe ba a ranar asabar da ta gabata 25 ga watan fabrairu.