Kungiyar tattallin arziki ta Africa ta yamma ECOWAS ta taya Asiwaju Bola Ahmad Tunubu murnar lashe zaben shugabancin Najeriya.

ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Abuja mai daken bunkasa zaman lafiya, Shugaban Kungiyar Umaru Sissoco Embalo, sanarwar ta kuma bukaci al-ummar kasar da su zauna da juna lafiya tare da bukatar sabon shugaban ya tabbatar ya yi wa duk jama’ar kasar adalci ba tare da nuna ban-bancin kabila ko addini ba.

A cikin wani labari mai kama da wannan, Sakataran gwamnatin tarayya Boss Mustapha a madadin gwamnatin tarayya da majalisar zartaswa ta kasa ya taya sabon Zababben shugaban Najeriya Asiwaju Bola Tunubu murnan lashe zaben kasar.

Mustapha ya kara da cewa Tunubu mutum ne kwararre ta fuskar mulki da tattalin arziki wanda kuma kwararre ne ta fuskar siyasa.

Mai gida Mustapha ya kuma yi kira ga al’ummar kasar da su gujewa tayar da hankula domin a cewarsa hakan ba abu bane mai kyau kuma bazai haifarwa kasar da mai ido ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: